1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Rasha za su karfafa dangantaka.

August 18, 2018

Shugabannin Jamus da Rasha sun jaddada kudirinsu na hada hannu domin kawo karshen rikicin Siriya da kuma tabbatar da masalaha a tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.

https://p.dw.com/p/33NBA
Deutschland Treffen Angela Merkel Wladimir Putin auf Schloss Meseberg
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce rikicin da yanzu haka ke wakana a Siriya da dambarwar da ake a gabashin Ukraine da kuma takun sakar Amirka da Iran na kan sahun gaba kan batutuwa da ita da takwaranta na Rasha Shugaban Putin na Rasha za su maida hankali a kai.

Baya ga wadannan batutuwa, Merkel ta ce ta tabo batun kare hakkin dan Adam a kasar Rasha da kuma ma kuma dangantaka da ke akwai tsakanin kasashen biyu wanda ke da karfin fada a ji a duniya.

Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce a ganinta abubuwa masu sarkakiya na bukatar a hau kan teburin tattaunawa a kuma yi amfani da masalaha wajen warwaresu. Wannan ne ma ya sanya ta ce ta ga dacewar tattaunawa kan wadanan batutuwan da shugaban na Rasha a ziyarar ya kawo a Jamus.