1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da Hollande da Renzi

Gazali Abdou TasawaJune 27, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta karbi bakuncin Shugaban Faransa Francois Hollande da kuma Firaministan Italiya Matteo Renzi domin nazarin fitar Birtaniya daga EU

https://p.dw.com/p/1JE6n
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/H. Hanschke

Kwanaki hudu bayan da 'yan Birtaniya suka zabi ficewa daga Kungiyar Tarayyara Turai wato EU, a yanzu haka kasashen Turai na ci gaba da nazarin hanyoyin diplomasiyya na gaggauta daukar matakan aiwatar da matakin raba gari da Birtaniyar da kuma na ceto kungiyar ta EU. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta karbi bakuncin shugaban kasar Faransa Francois Hollande da kuma Firaministan Italiya Matteo Renzi a Birnin Berlin fadar gwamnatin kasar, da nufin yin nazari dangane da ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai gabanin taron koli na kungiyar ta EU da za su gudanar a ranar Talata 28 ga wannan wata na Yuni da muke ciki, inda kasashen Kungiyar za su tattauna kan matakan da suka dace su dauka domin sake farfado da matsayin kungiyar bayan ficewar Birtaniyan.