Mbeki ya yabawa jamus
July 9, 2006Talla
MBEKI
Shugaba Thabo Mbeki na kasar Afrika ta kudu yayi maraba da kokarin rundunar sojin Jamus wajen taimakawa samar da zaman lafiya a janhuriyar Democradiyyar Congo.Shugaban na Afrika ta kudu yace samarda zaman lafiya a Sudan da Congo ,nada matukar mihimmanci a zamantakewar nahiyar Afrika baki daya.Kimanin dakarun sojin Jamus 800 ne,zasu kasance a kasar janhuriyar democradiyya Congo,a bangaren kokarin da kasashen duniya keyi na samar da zaman lafiya da tsaro lokacin zaben kasar da zaa fara ranar 30 ga wannan wata.