1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi da Nijar za su ƙaddamar da hari kan Boko Haram

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 8, 2015

Wata majiya daga gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewar jami'an sojan ƙasar da takwarorinsu na Chadi za su ƙadddamar da hari ta sama da ta ƙasa kan mayaƙan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1EnLB
Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Chadi da ke yaki da Boko HaramHoto: Reuters/E. Braun

Ƙungiyar ta Boko Haram dai na yin gwaggwarmaya da makamai a maƙwabciyar ƙasashen na Chadi da Nijar ɗin wato Tarayyar Najeriya. Majiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasar Faransa na AFP cewar za su ƙaddamar da gaggarumin farmakin a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriyar da ƙungiyar take da ƙarfi wanda kuma ke kan iyaka da garuruwan Bosso da Diram. Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da aka kai wani mummunan hari a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a Tarayyar Najeriya tare da hallaka mutane sama da 50.