Rufe iyakokin Najeriya ya janyo cikas
September 19, 2019Talla
Matakin rufe kan iyakokin Najeriya da mahukuntan kasar suka yi bisa dalilai na magance fasa kwaurin kayan abinci musamman shinkafa 'yar waje da kuma duba batun tsaro, ya haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci da ma zirga-zirgar jama'a tsakanin Najeriya da kasashe makwabtanta.