Cece-cuke kan rufe iyakokin Najeriya | BATUTUWA | DW | 17.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Cece-cuke kan rufe iyakokin Najeriya

Hukumomin Najeriya sun jaddada dalilan rufe iyakokin kasar da ‘yan kasuwa a Najeriya da ma kasashen makwabta suka game da cikas da matakin gwamnatin kasar ya haifar.

A  lokacin da ‘yan kasuwa a Najeriya da ma kasashen makwabta ke kuka game da cikas din da rufe kan iyakokin kasar da gwamnatin Najeriya ta yi, hukumomin kasar sun bayyana dalilan yin haka da masana tattalin arziki ke kalon akwai sauran gyara a daukacin lamarin.

Gwamnatin Najeriya dai tana ci gaba da aiwatar da rufe kan iyakokin a yanayi na sintirin hadin gwiwa da jami’an tsaro da na binciken shige da ficen jama’a ke yi, abinda suka bayyana a matsayin mataki na dakile masu fasa kwaurin kayan abinci musamman shinkafa daga kasashen makwabta da ma dalilai na yanayin tsaro. To sai dai ‘yan kasuwa a Najeriyar da kasashen ketare na bayyana cewa suna fa tafka mumunar asara a dalilin wannan mataki.

Ta kai ga zargi na saba kudurin kungiyar Ecowas da ya ba da izini kai da komo na jama'a, amma ga  Mr Joseph Attah mataimakin kontrola ne a hukumar kwastom kuma kakakin hukumomin da ke sintiri a kan iayakokin Najeriya.

Najeriya dai na da ‘yan kasuwa da ke kai da komo a tsakanin kasashen yankin Afrika ta Yamma. Sanin cewa Najeriya ta dage a kan batu na tsaro a matsayin daya daga cikin dalilan rufe kan iyakar, ko zuwa yanzu sun kama wasu makamai a kan iyakaokin nata.

Da alamun dai kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sai dai su bi hanyar da ta shimfdida, domin tuni Jamhuriyar Nijar ta bayyana hana barin duk wata shinkafa ta ratsa ta kasarta zuwa Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin