Masar ta yi gargadi ga masu zanga-zanga
October 5, 2013Mai magana da yawun fadar mulkin kasar Ahmed al-Muslimani ne ya bayyana hakan a wannan Asabar din, kwana guda kafin cika shekaru arba'in da samun nasarar da Masar ta yi kan wani hari da suka kai wa sojin Isra'ila a wani yaki da suka gwabza.
Mr. al-Muslimani ya ce dukannin wanda ya yi kunnen kashi game da wannan gargadi da gwamnatin kasar mai samun goyon bayan soji ta yi, to shakka babu za su dauke shi a matsayin wanda wasu kasashen ketare ke mara wa baya wajen tada zaune a Masar.
Wannan sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da 'yan jam'iyyar 'yan Uwa Musulmi ta hambararren shugaba Muhammad Mursi suka lashi takobin bazama kan tituna a wannan Lahadi domin nuna fushinsu ga sojin kasar wanda suka hambarar da gwamnatin Mursi watannin da suka gabata.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal