Martanin ′yan siyasan jamus akan zaɓen jihohi | Siyasa | DW | 28.01.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin 'yan siyasan jamus akan zaɓen jihohi

Sakamakon zaɓe a jihohin Hesse da Lower Sasony ya haifar da mahawara

default

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel

Duk da kaye da ɗumbin asarar ƙuri'u da jamiiyyarta ta CDU tayi a zaɓen daya gudana jiya lahadi a jihohi biyu,shuagbar gwamnati Angela Merkel ta lashi takobin cewar sakamakon zaɓen bazai haifar da cikas cikin gwamnatin hadin kan kasa da take wa jagoranci ba. Zaɓen daya gudana a jihohin Hesse da Lower Saxony a jiya lahadi,na mai zama wani sabon babi a harkokin siyasar tarayyar jamus,musamman a bengaren manyan jami'iyyu biyu dake jan ragamar mulki a tarayyar Jamus. A jihar Lower Saxony,dake yankin arewa maso gabashin ƙasar,Primiya Wulff na jami'iyyar CDU cimma zarcewa kan kujerar mulkin sa a gwamnatin hadaka da yake yi da jami'iyyar FDP,duk dacewa ya fuskanci koma baya ta ɓangaren magoya baya. Kazalika labarin ba daban yake da Jihar Hesse ba,inda nan Premier Roland Koch na jami'iyyar CDU ta Merkel yasha dakyar,daga jami'iyyar masu sassaucin ra'ayi ta SPD,koda yake ya samu karin magoya baya da kashi 12 daga cikin 100 idan aka kwatanta da zaben karshe daya gudana a 2003. A taron manema labaru data gudanar Shugabar gwamnatin jamus kuma shugabar jami'iyyar CDU,Angela Merkel tace duk da irin ɗumbin asara da jami'Iyyar ta tayi a jihohin Lower Saxony da Hesse,tana da imanin cewar suna da karɓuwa fiye da takwarar su ta SPD. "A jihar Lower Saxony,sakamon zaɓen ya bayyana yadda jami'iyyar SPD ta samu koma baya sosai a karon farko,tun daga shekara ta 1947,kuma kusan haka samakon yake a jihar Hesse.A yanzu haka zamu iya cewa,duk da asara da mukayi ,wanda ke zama babban bakin ciki ne a bangaremmu, jamiyyar CDU har yanzu itace keda karfi a dukkannin jihohin biyu" Shi kuwa shugaban jami'iyyar SPD na kasa Kurt Beck,yace zasu cigaba da taka rawa wajen cimma manufofin da suka sa gaba a cikin sauran wa'adin mulkin haɗaka da sukeyi da takwarra su ta CDU. "Har yanzu muna kan manufofin mu dangane da samun nasara ta fannin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da adalci ta fannin rayuwa,kazalika a sauran wa'adin mulkimmu daya rage" To sai dai wasu 'yan siyasan na ganin cewar wannan matsayin da manyan jami'yyu biyun suka tsinci kansu ciki wani batu ne dake nuna sauyi cikin guguwar siyasar tarayyar jamus.inda jamiiyyar masu ra'ayin gurguzu suke cigaba da samun nasara da wakilci a majalisun jihohin yammacin jamus. Gregor Gysi shine kakakin 'yan majlisa masu ra'ayin gurguzu a majalisar tarayyar ƙasar. "Yace wannan babban nasara ce a ɓangaremmu.Kuma daga yanzu dole ne sauran suyi alakar tsarin irin na jami'iyyu biyar.,wanda hakan ne zai kawo ruɗani tsakanin su ,kuma irin saɓani mai tsanani zai haifar"
 • Kwanan wata 28.01.2008
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CytD
 • Kwanan wata 28.01.2008
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CytD