Majalisar dokokin yankin Palasdinawa ta fada cikin rudani | Labarai | DW | 07.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin yankin Palasdinawa ta fada cikin rudani

Rahotanni daga yankin Palasdinawa na nuni da cewa yan majalisar dokokin yankin sun tashi daga zaman zauren majalisar na farko a cikin rudani.

Hakan dai ya faru ne bayan da yan majalisar dokokin na kungiyyar Hamas suka hau kujerar nakin kin amincewa da wasu kudurori da majalisar data gabata ta zartar .

Daga cikin kudurorin kuwa akwai batun bawa shugaba Mahmud Abbas ikon nada alkalan kotun koli na yankin.

Ya zuwa yanzu dai tuni yan majalisar dokokin na jamiyyar Fatah suka ce takwarorin nasu daga kungiyyar Hamas basu da ikon kawo wani canji, a game da matakan da majalisar farko ta aiwatar.

A waje daya kuwa, kungiyyar ta Hamas tace tana da ikon hakan , bisa dalilin cewa majalisar ta farko ta gudanar da zaman nata ne makonni biyu bayan gudanar da zaben daya basu nasara.