Majalisar Dinkin Dunia ta yi shelar tallafawa Somalia
December 14, 2005Majalisar Dinkin Dunia, ta tara kokon bara, da burin tattara a kalla, dalla million 174 domin bada taimakon raya kasa ,ga Somalia, da ke fama da yake yake, tun shekara ta 1991.
Wakilin Majalisar DinkinDunia mai kulla da Somalia, a wani taron manema labarai, da ya shirya ya bayana cewa a halin da a ke ciki fiye da mutane dubu dari 3 ,ke fama da matsananciyar yinwa a wannan kasa, a yayin da mutane dubu dari 4 su ka shiga uwa dunia, don tsira da rayukan su, a sakamakon hare hare da yake yaken bassasa, da ke ci gaba da wakana.
Munate da su ka rugumi kaddara, su ka tsaya a gidajen su, na fama da cuttutuka daban daban da rashin aikin yi, da taka hakoki, ta fannoni da dama.
A shekara da ta gabata an girka sabin hukumomi a kasar, to amma ,su na fama da rabuwar kanu, abinda ke jawo cikas, ga ci gaban da ake bukatar samu.
Yakin Somalia, ya hadasa mutuwar mutane dubu dari 3 zuwa dubu 5, inji alkalumman Majalisar Dinkin Dunia.