Majalisar dattijan Amurka ta amince da nadin sabon sakataren tsaron Amurka | Labarai | DW | 07.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattijan Amurka ta amince da nadin sabon sakataren tsaron Amurka

Majalisar dattijan Amurka ta amince da nadin Robert Gates a matsayin sabon sakataren tsaro na Amurka wanda zai maye gurbin Donald Rumsfeld da yayi murabus a watan daya gabata .

Kuriu 95 aka kada na amincewa da nadin Gates yayinda 2 suka ki amincewa da shi.

Tun ranar talata komitin harkokin tsaro na majalisar ya amince baki dayansa game da nadin gates.

Tun farko Gates ya fadawa membobin komitin cewa bai yarda cewa Amurka tana samun nasara a Iraqi ba haka kuma yayi gargadin cewa yakin Iraqi zai iya bazuwa zuwa yaki a yankin baki daya.