Majalisar dattijan Amurka ta amince da dokar Bush akan wadanda ake zargi da taaddanci | Labarai | DW | 29.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattijan Amurka ta amince da dokar Bush akan wadanda ake zargi da taaddanci

Majalisar Dattijan Amurka ta amince da kudirin doka nan game da hanyoyi yiwa wadanda ake zargi da taaddanci tanbayoyi.

Dokar dai a karkashinta zaa dauki tsauraran mataki wajen tambayar wadanda ake ganin yan taadda ne.

A ranar laraba ne kuma majalisar wakilai ta amince da irin wannan doka.

Hakazalika majalisar ta wakilai ta sake amince da ci gaba da tabo maganganun wayar tarho na yan kasar Amurka karkashin yakinta da taadanci.

Har ya zuwa farkon wannan shekara da wannan batu ya janyo suka daga jamaar kasar.

Bush a nasa bangare yace a matsayinsa na shugaban kasa yana da iko karkashin kundin tsarin mulkin kasar ya tabo tarho din ba tare da neman iznin kowa ba.