1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Menene makomar zabukan 2023?

June 1, 2021

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kona ofisoshin hukumar zabe a sassan kudancin Najeriya, shugabannin hukumar zaben ta INEC sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari da nufin neman mafita.

https://p.dw.com/p/3uJRt
Nigeria Prof. Mahmoud Yakubu (L) Präsident Muhhamadu Buhari
Shugaban hukumar INEC Mahmoud Yakubu da shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Imago/Zuma

Ya zuwa yanzu dai akalla ofisoshin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC a Najeriyar 42 ne aka kona, a sassa dabam-dabam na  kasar tun bayan zaben 2019. To sai dai kuma mafi  daukar hankali na zaman jerin harin da ke zaman salo a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar, daya kalli kona ofisoshi dai dai har 12  cikin tsawon makonni biyu a wani abu da ke zaman karuwar ta'azzarar hari na cibiyoyi na hukuma. Karuwar harin dai ya tilastawa shugabancin Hukumar Zaben mai Zaman Kanta na kasa baki daya, ganawa da shugaban kasar domin neman mafita.

Karin Bayani: Barazarar tsaro ga zabukan 2023 a Najeriya

Tun a makon jiya dai shugabancin na INEC ya gana da manyan jami'an tsaron da ke aikin zaben, da nufin nazarin matsalar da ke iya kai wa ga jefa kasar cikin rikicin zabe. Ana dai kallon ganawar da shugaban kasa, a matsayin wani sabon yunkuri na hukumar da ga dukkanalamu na bukatar sababbin kayan aiki da kila ma karin kason kudi da nufin iya kai wa ga rage radadin rashin tsaro.

Nigeria - Wahl verschoben
Bukatar karin kudi da kayan aiki ga hukumar zaben Najeriya wato INECHoto: Reuters/S. Maikatanga

To sai dai kuma  shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na shirin bai wa hukumar zaben daukacin abun da take da bukata, domin tabbatar da hukumar ta INEC ta gudanar da zabukan a ko'ina komai rintsi. Buharin dai ya ce yana samun rahotanni na harin a kusan kullum ya ce masu kai harin suna shirin shan mamaki bayan doguwar igiya ta gwamnatin don rataye kansu.

Karin Bayani: Yabo ga INEC kan gudanar da zaben Edo 

A watan Nuwambar da ke tafe ne dai, INEC din ta tsara zaben gwamnan jihar Anambra daya a cikin jiohin na Kudu maso Gabas, ko bayan fara shirin sake rijistar masu zabe na kasar a ranar 28 ga watan Junin da muke ciki. To sai dai kuma a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Abuja, jihohin na Kudu maso Gabas ba su da yawan da za su iya jawo cikashi ga karbuwar zaben a cikin kasar baki daya. Abun jira a gani dai na zaman tasirin rikicin ga batun zaben da kila ma makomar dimukuradiyya a cikin Najeriyar.