1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tattaunawa kan matsalolin zabe

Uwais Abubakar Idris AH
July 3, 2019

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta kammala wani taro da kungiyoyin farar hula inda ta duba dimbin matsalolin da ake fuskanta a harakar zabe.

https://p.dw.com/p/3LXH8
Nigeria Regionalwahlen 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Wannan taro da hukumar ta INEC ta shirya ga masu ruwa da tsaki a harakar zaben Najeriyar da kungiyoyin farar hula da suke saka ido a kan zaben don bayyana wa juna gaskiyya a kan abubuwan da ke faruwa wadanda ke bukatar gyara. A zabbukan baya dai a Najeriya an yi ta samun kura-kurai,kama daga aringizon kuri’u zuwa ga sace akwati baya ga wadanda suka tada hankali ta hanyar rigingimu, batun gyara da samun ci gaba ya zama kan gaba a taron. A karshen  taron dai an fadakar da wakilan kungiyoyin dabam-dabam yadda za su iya tinkarar sha'anin zaben domin magance matsalar da ake fuskanta a lokutan zabukan a Najeriya.