An yaba wa hukumar INEC bisa nasarar gudanar da zaben gwamnan jihar Edo | Siyasa | DW | 21.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An yaba wa hukumar INEC bisa nasarar gudanar da zaben gwamnan jihar Edo

Zaben gwamna a jihar Edo ya dauki hankula 'yan siyasar Najeriya da masharhanta a matsayin zakaran gwajin dafin jam'iyyun APC da PDP.

'Yan siyasar jihar ta Edo, da abokanansu na sauran sassan kasar da suka je musu kai dauki, sun matsa kaimi matuka wajen firgita masu kada zabe a jihar ta hanyar ta da hankula. Sai dai kuma bisa ga abin da ya faru, hakan bai yi tasiri kan jajircewar ma su kada kuri'a a Edon ba, domin kuwa sun fito sun kada wa wadda suke so.

Wata 'yar Edo, da ke cikin farin ciki ga sakamakon zaben cewa ta yi "cike nake da farin ciki, kuma jajircewar da muka yi don ganin Godwin Obaseki ya dawo ba karama ba ce, mai duka ya yi mana komai, gaskiya ina farin ciki."

Al'ummar jihar ta Edo dai sun yi farin cikin da yadda sakamakon zaben ya kasance

Al'ummar jihar ta Edo dai sun yi farin cikin da yadda sakamakon zaben ya kasance

Zaben dai da ya gudana ba da wani babban tashin hankali ba, kamar yadda aka yi ta tsammani, nan da nan ne, fadar shugaban kasar Najeriya ta fito ta yaba yadda aka gudanar da zaben, k kuwa da cewar jam'iyyar adawa ta PDP ce ta lashe zaben. Sai dai kuma jam'iyyar shugaban kasar ta APC a jihar ta Edo ta yi watsi da sakamakon zaben.

Da dama dai na kallon kokarin hukumar zaben kasar a yanzu, bisa yadda zaben na Edo ya kasance, ganin cewar dukkanin tsare-tsarenta sun gudana cikin nasara.

Duk da kokarin da Adams Oshiomhole ya yi na ganin APC ta lashe zaben, hakan bai tabbata ba

Duk da kokarin da Adams Oshiomhole ya yi na ganin APC ta lashe zaben, hakan bai tabbata ba

Rawar da gaggan 'yan siyasar kasar suka taka dai a wannan zabe, musamman ma na jam'iyyar APC mai mulki, bisa ma la'akkari da cewar Comrade Adams Oshiomhole, wanda tsohon gwamnan jihar ta Edo ne, kuma tshohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, tare da tallafawar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, hakan bai sa sun kai gaci ba.

Wani Dakta Ahmad Umar kan yi sharhi kan siyasa a kasar, kuma ya ce darasin da ya bayyana na shugabanni ne.

Barista Jalo, wani kusa a jam'iyyar ta APC kuwa cewa ya yi abin da ya faru, faduwa ce ga jam'iyyar ta APC a zabukan kasa na shekarar 2023 mai zuwa.

Koma dai ta yaya za a fassara siyasar jihar ta Edo a yanzu, wani Mr Raphael da ke da jibi da mutanen Edo din cewa ya yi, al'ummar jihar sun bayyana matsayarsu a siyasance da kuma kowa ke gani, don haka ma su siyasar uban gida, sai dai su koma gefe guda.

Sauti da bidiyo akan labarin