1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro zai shafi zabukan 2023

April 30, 2021

Babbar jam'iyar adawa ta PDP ta ce, da kamar wuya zabe ya iya gudana a 2023 cikin yanayi na tsanantar rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu.

https://p.dw.com/p/3snxP
Nigeria Polizeikräfte in Lagos
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

A takarda dai tuni hukumar zaben kasar ta INEC ta saka ranar 18 ga watan Fabrairu na shekara ta 2023 a matsayin ranar zaben shugaban kasa a tarrayar Najeriya.

Kuma ma an yi nisa a bangaren masu siyasar da ke kace-nacen juyawar mulkin ya zuwa sassa daban daban da ke da tunanin ko nasu ko kafar katako.

To sai dai kuma a karon farko, jam'iyar PDP mai adawata ce masu tunanin zaben na kama da masu mafarki da tsakar rana cikin kasar da ke kokarin kisan wutar rashin tsaro a halin yanzu.

Nigeria Femi Fani-Kayode
Wasu 'yan jam'iyar PDP lokacin taron kasaHoto: AFP/Nan Photo

Babban taron jam'iyyar na kasa dai ya ce da kamar wuya a iya kaiwa ga batun zaben a cikin halin ta'azzarar rashin tsaron da ta mamaye daukaci na sassa na kasar.

A tunanin 'yan lemar dai babu kudu, balle arewacin kasar cikin batun zaman lafiya da a cewar Senata Umar Ibrahim Tsauri da ke zaman sakataren jam'iyyar na kasa, ke zaman sharadin farko na tabbatar da kadin kuri'ar a ko'ina.

Karin bayaniPDP da APC sun fafata a zaben Ondo

Magudi cikin rashin tsaro, ko kuma rudani ga kasar da ke da tsarin mulki na shekaru hudu, rashin tsaron dai na dada daukar hankalin 'yan mulkin da ke fadin sun yi nisa a cikin neman mafitar rikicin.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Kuma a fadar Barrister Ismael Ahmed da ke zaman kakakin jam'iyyar APC na kasa masu tsintsiyar basu da tarihin dage zabe bisa batun rashin tsaron, balle a iya kaiwa ga magudi cikin yanayin maras kyau.

Karin bayani: Zaben kananan hukumomi: Nadi ko zabe?

Najeriyar dai na da tarihi na  zabuka cikin halin rikici, kuma ma a fadar farfesa Mustapha Osuji da ke sharhi kan harkokin tsarin mulki da siyasar kasar, tada hankali yayin zabe na zaman salo irin na siyasa ta Najeriyar a lokaci mai nisa.