Macron da Merkel na son warware rikicin bakin haure | Siyasa | DW | 28.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Macron da Merkel na son warware rikicin bakin haure

Shugabannin kasashen Turai na halartar taro a birnin Brussels don dakile kwararar bakin haure daga tekun Baharum tare da karfafa tsaro na gadin gabar tekun Italiya domin hana jiragen 'yan ci rani tsallakawa zuwa Turai.

Sakamakon haramci da yin watsi da jiragen ceton 'yan ci ranin da ake samu a gabar teku, ana ci gaba da nuna damuwa a sahun kungiyoyi masu aikin ceton da kuma Coci da ke yin Allah wadai da abin da suka kira rashin imani. A share daya kuma 'yan siyasa na kasashen Spain da Italiya da Faransa da Malta suke ci gaba da yin muhawara dangane da wadanda ya kamata su rika yin aikin ceton da jiragen ruwa.

Tun farko dai Italiya ta ja da baya a game da kudirin da ta amince da shi a farkon wannan shekara ta 2018 na karbar bakin haure don basu mafaka ga wadanda aka ceto daga tekun Meditraneen. Kuma saobn ministan cikin gida na Italiya na bangaran jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya Matteo Salvini ya ce ba za su kara barin jiragen ceton ba dauko bakin hauren suna shigo masu da su a cikin kasarsu wanda kuma ya ce lokacin jin gatanci na 'yan cirani ya kare.  

Matteo Salvini

Ministan cikin gidan Italiya Matteo Salvini ya tsaurara matakan yaki da 'yan gudun hijirar Afirka

 

Sai dai Michael Buschheuer shugaban kungiyar aikin ceton 'yan ciranin ta Sea Eye ya ce furucin ministan na cikin gida na Italiya bai basu mamaki , inda ya ce "wadannan halaye yau sama da shekara guda ke nan muke ganin irinsu tun a cikin watan Maris na shekara ta 2017. dukkanin kasashen Turai na neman maraba da kungiyoyin masu aikin ceto a gabar Teku wanda  ake neman saka musu birki ta hanyar matakan da ake dauka na janyo musu cikas"

Kasashen na Turai na neman a dakatar da aikin kungiyoyin masu jiragen ceton wadanda suke zargi da hada baki da masu yin fasa kwabri na 'yan cirani  domin tsallaka Tekun da su daga Libiya. Dangane da haka ne wani alkalin bincike ya gudanar da bincike a Palermo da Siciliya. Sai a makon jiya ya kammala bincike wanda bisa ga dukkan alamu ya bayyana cewar babu shaidu na zargin da ake yi wa kungiyoyin.

Cibiyar da ke kula da gadin iyaka ta Frontex ta sha yin suka game da wani irin safara da ake yi na 'yan ci ranin wanda a kan biya miliyoyin daloli don shiga cikin jiragen ruwa marasa inganci ko ma na roba ko na katako da ake tsalllaka tekun da su.

 Micheal Buschheueur ya ce akwai bukatar a bar kungiyoyin masu aikin ceton da su ci gaba da yin aikinsu, inda ya ce '' Idan muka daina yin wannan aiki a yanzu mu kungiyarmu da ma sauran kungiyoyi, to babu shakka zai zama abu mafi sauki ga masu gadin tekun na yin watsi da masu bukatar ceton"

Libyen Migranten aufSchlauch von Schiff der deutschen NGO Mission Lifeline gerettet

Alkaluma sun nunar da cewa 'Yan gudun hijirar Afirka da ke shiga Turai sun ragu

Shugabannin kasahshen Turan wadanda ke yin taron a birnin Brussels na kokarin ganin sun dau matakai na hana 'yan ci rani ketarwa ta barauniyar hanya ta tekun Mediteraneen domin shiga Turai, hanya mafi hatsari da ake samun asarar rayuka. Italiya dai  ta cimma wata yarjejeniya da gwamnatin Libiya da ma watakila kungiyoyin mayakan sa kai cewar su rika tare 'yan ci rani su kuma basu kudade.

Hukumar kaura ta Majalisar Dinkin Duniya OIM ta ce adadin wadanda ke ketare tekun na Bahatrum zuwa Italiya ya ragu a cikin watannin shida na farkon wannan shekara da mutum dubu 16400, yayin da a bara ya kasance mutum dubu 73000 a watanin shida na farko kuma a wannan shekara mutane akalla 635 ruwa ya cisu tsakanin Libiya da Italiya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin