1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron neman mafita ga kasar Libiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 12, 2021

Ana sa ran manyan kasashen duniya su bayyana aniyarsu ta kakaba takunkumi ga duk wani da ya yi kokarin kawo kafar ungulu, a kokarin samo mafita ga kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/42wGb
Spain Migration
Rikicin Libiya ya janyo asarar rayuka da dama, kana dubbai sun fantsama gudun hijiraHoto: picture-alliance/AP Photo/O. Calvo

Gargadian dai za su yi shi ne musamman kan yyiwuwar dakile kokarin yin zabe tare da mayar da mulkin Libiya zuwa kan turbar siyasa. Ana sa ran kasashen su bayyyana wannan aniyar tasu, a karshen taronsu na birin Paris fadar gwamnatin kasar Faransa domin nemo mafita ga Libiyan. Taron wanda zai samu halartar shugabannin kasashen Faransa mai masaukin baki da Libiyan da Jamus da Masar, ana kuma sa ran mataimakiyar shugaban kasar Amirka Kamala Harris za ta wakilci kasarta.

Yayin tgaron dai, shugabannin za su bayyana goyon bayan kasashen duniya ga babban zaben Libiyan da za a gudanar a ranar 24 ga watan Disambar da ke tafe da kuma kokarin ganin sojojin kasashen waje sun fice daga kasar. Zaben na zaman wani babban jigo cikin matakan da Majalisar Dinkin Duniya ke dauka a Libiya, domin kawo karshen yaki da tashe-tashen hankulan da aka kwashe tsahon shekaru 10 ana fama da shi a kasar. Tun bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta taimaka wajen kifar da gwamnatin marigayi shugaban kasar Libiyan Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, Libiya ta shiga cikin halin tasku.