1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Lauyoyin Bazoum sun bukaci ECOWAS ta nemi sakinsa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 24, 2024

A cikin watan Disamban bara ne dai kotun ECOWAS ta bai wa sojojin da ke mulki a Nijar umarnin sakin Bazoum tare da mayar masa da mulkin kasar

https://p.dw.com/p/4cpJM
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Lauyoyin hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum sun bukaci kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da ta nemi sojojin da ke tsare da shi su sake shi.

Karin bayani:An kama tsohon minista a Jamhuriyar Nijar

Rokon na zuwa ne a daidai lokacin da ECOWAS din ke taron ta na koli a Asabar din nan a Abuja babbar birnin Najeriya, domin nazartar halin da yankin ke ciki.

Karin bayani:Kotu ta saki dan Bazoum Mohammed

A cikin watan Disamban bara ne dai kotun ECOWAS ta bai wa sojojin da ke mulki a Nijar umarnin sakin Bazoum tare da mayar masa da mulkin kasar.

A farkon watan Janairun da ya gabata ne sojojin suka saki 'dan Bazoum Salim, amma suka ci gaba da tsare shi da mai dakinsa a fadar mulkin kasar.