Nijar: Kotun soji ta saki dan Bazoum Salem
January 9, 2024Talla
A cewar wani hukunci da kotun sojan Yamai ta yanke wanda kamfanin dillancin labaran na Faransa AFP ya bayyana ya ce Salem an yi masa sakin wucin gadi daga alkalin da ke bincike na kotun soji. Sannan kotun ta ce ya kasance cikin shiri idan shari'a na bukatarsa. Salem Bazoum, mai shekaru 23, ya bar Yamai zuwa Lomé.Togo dai ta kwashe makonni da dama tana ta yin tattaki domin shiga tsakani da gwamnatin sojan da ke kan madafun iko.