Jamus: Ko Merz na karkata zuwa kyamar baki?
November 11, 2025
Tuni masu suka, suka fara ayyana shugaban gwamnatin ta Jamus Friedrich Merz da wanda ke karkata ga bangaren masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki da kishin kasa. "Akwai matsaloli a kan yanayin yadda tsarin biranenmu yake, ku tambayi yaranku mata." A cewar Merz. Wadannan kalaman na shugaban gwamnatin Jamus, sun janyo cece-kuce.
Rabin al'ummar birnin na da alaka da baki
Ga misali birnin Nürnberg na dauke da yawan al'umma dubu 500, kuma kaso 50 cikin 100 na da nasaba da baki. Daga cikinsu akwai Nasser Ahmed da ke son zama magajin garin birnin na gaba. Ya bayyana takaicinsa kan kalaman na Merz yana mai cewa: "Kalaman kan yadda tsarin biranenmu yake, watsa kasa a ido ne ga miliyoyin mutane da suka sake gina kasar daga tushe bayan yakin duniya na biyu........ A ganina, ya kamata Merz ya nemi afuwa."
Karin Bayani: Jamus: Zare tallafin aikin ceto a Bahar Rum
Sai dai yayin da Ahmed ke ganin ya kamata Merz ya nemi afuwa saboda alakanta rashin tsaro da kwararar baki, kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna mutane da dama sun yadda da shugaban gwamnatin. A ganinsu bakin hauren da ba su da takardu ne matsalar, sai dai duk da haka wasu na ganin ana wuce gona da iri wajen yadda ake bayyana ta.
Wadannan kalamai sun dan taka rawa wajen kara karfi ga jam'iyyar AfD ta masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki da kishin kasa, inda a yanzu suke samun nasara a zabukan kasar. Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, shugaban bangaren jam'iyyar CDU a majalisar dokoki Jens Spahn ya nunar da cewa: "Muna da jam'iyyar da ke da mutane da dama masu rike da mukumai a cikinta da ke goyon bayan Vladmir Putin da Rasha da masu kyamar Yahudawa da kuma masu kyamar baki............ Hanyar da ta fi dacewa a ba su tabbacin akwai batun magance matsala, guda cikinsu ita ce batun 'yan gudun hijira."
Mafita ko matsala?
Sai dai masu gangamin yaki da tsattsauran ra'ayin kyamar baki kamar Stephan Doll na kungiyar Hadaka da ke Fafutukar Yaki da Tsattsauran Ra'yin Kyamar Baki da Kishin Kasa, na gargadin cewa wannan matakin na kama da abu mai kyau amma kuma yana iya yin mummunar illa. A nasa bangaren, Nasser Ahmed na fatan kalamansa na samun tsaftatacciyar siyasa za su taimaka masa yayin da al'ummar Bavaria suka fita kada kuri'unsu a watan Maris din shekarar da ke tafe ta 2026.