Kungiyyar tsaro ta Nato ta mika goron gayyata ga kasashen Balkans | Labarai | DW | 29.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyyar tsaro ta Nato ta mika goron gayyata ga kasashen Balkans

Shugabannin kungiyyar tsaro ta Nato, sun amince da matakin farko na shigo da kasashen Serbia da Bosnia da kuma Montenegro, a matsayin mambobin ta.

A cewar shugabannin na Nato, kungiyyar ta yanke daukar matakin ne don irin gudummawar da kasashen zasu bayar wajen samun zaman lafiya a yankin Balkans.

Bugu da kari kungiyyar ta Nato ta kuma tabbatar da cewa, matakin zai taimaka wajen yadda kasaashen Serbia da kuma Bosnia zasu dakile faruwar miyagun ayyuka a yankin.

A karshe, shugabannin na Nato sun kuma shaidarwa kasashen Albania da Croatia da kuma Macedonia, cewa matukar suka cimma sharudan kungiyyar to suma zasu sami goron gayyata na shiga cikin yayan kungiyyar, watakila a taron kolin kungiyyar na shekara ta 2008.