Kungiyar EU na kara shiri kan tsaro | Labarai | DW | 20.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU na kara shiri kan tsaro

EU ta shirya tura wasu jami'an tsaro da zasu yi aiki na tallafawa shirin karya lagon shirye-shiryen ta'addanci, musamman a kasashen da ake samun masu tsatsauran ra'ayi.

EU Arabische Liga Treffen Federica Mogherini mit Nabil al-Arabi

Nabil al-Arabi na kungiyar kasashen Larabawa da Federica Mogherini ta Kungiyar EU

Kungiyar Tarayyar Turai na kara daukar matakan hadin kai na tsaurara tsaro da kasar Turkiya da ma wasu kasashen Larabawa.

Bayan kammala taro da mambobin kungiyar kasashen Larabawa a jiya Litinin shugabar shirin harkokin kasashen waje daga kungiyar ta EU Federica Mogherini, ta bayyana cewa kungiyar ta EU ta shirya tura wasu jami'an tsaro da zasu yi aiki na tallafawa shirin karya lagon shirye-shiryen ta'addanci.

Ta ce domin tabbatar da ganin dorewar dangantakar tsakanin su da kasashen na Larabawa zasu kafa wani shiri mai tsari da za a rika bibiya. Nan gaba kadan ne kuma cikin makonni zasu kaddamar da wasu aikace-aikacen a wasu kasashe da suka hadar da Turkiya da Masar daYemen da Aljeriya da kasashen yankin Gulf.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu