Kungiyar Alqaeda ta lashi takobin kai manyan hare hare | Labarai | DW | 11.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Alqaeda ta lashi takobin kai manyan hare hare

Kungiyar Aqaeda a Iraki a yau lahadi ta lashi takobin kai manyan hare hare wadda tace zasu gurgiza abokan gabanta,bayan kashe shugabanta na Iraqi Abu Musab alzarqawi.

Cikin wani sako ta yanar gizo,kungiyar tace manyan jamianta sunyi taro bayan kashe Zarqawi domin tattauna hanyoyin da zata maida martani tare kuma da sabunta mubayaarsu ga Osama Bin Laden.

Sanarwar tace hare hare da suka shirya kaiwa zasu matukar girgiza abokan gaba tare da hanasu runtsawa,saboda abinda suka aikata.