Kotu a Libya ta tabbatar hukuncin kisa kan wadanda sukayiwa yara allurar kamuwa da kanjamau | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Libya ta tabbatar hukuncin kisa kan wadanda sukayiwa yara allurar kamuwa da kanjamau

Wata kotu a kasar Libya ta tabbatar da hukuncin kisa kann wasu maaikatan jiya 5 yan kasar Bulgaria da wani likita Bapalasdine wadanda ake zarginsu da cewa da gangan sukayiwa wasu yaran Libya kusan 400 allurara kawayr cutar kanjamau.

Tun a shariar farko dai aka yankewa wadannan mutane 6 hukuncin kisa a Benghazi a 2004,to amma kotun koli ta Libyan ta bada umurnin sake sauraron karar bayan kiraye kiraye daga kasashen yamma.

Iyalan yaran da abin ya shafa sun gudanar da zanga zanga na nuna amincewarsu da wannan hukunci da aka yanke.

Kodayake masu lura da alamura na yammam sunce anyi anfani da wadannan mutane ne don kare abinda suka kira gazawar hukumomin lafiya na Libya.

Kasashen duniya da dama dai sunyi Allah wadai da wannan hukunci.