Koriya ta kudu ta amince ta lalata dukkan shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 03.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta kudu ta amince ta lalata dukkan shirinta na nukiliya

Koriya ta kudu ta amince ta baiyana tare da lalata dukkanin kayayyakinta na nukiliya nan zuwa karshen shekara da muke ciki.Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Christopher Hill ya sanarda da haka a karshen tattaunawarsa na kwanaki biyu da jamian Koriya a Geneva.Yace ganawar tsakanin jamian Koriya ta kudu dana Amurka ya taimaka inganta hanyoyin samun nasara a tattaunawar da zasu yi nan gaba cikin wannan wata.Wao lokacinda bangarorin biyu zasu gana da kasashen Japan da rasha da Koriya ta arewa da China a kokarinyu na ganin Koriya ta dakatar da shirinta na nukiliya tare da inganta dangantakun diplomasiya tsakanin Koriya ta kudu da sauran alummomin duniya.