Komitin sulhu ya amince aikawa da dakarun majalisar dinkin duniya zuwa Sudan | Labarai | DW | 03.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya amince aikawa da dakarun majalisar dinkin duniya zuwa Sudan

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya baiwa Majalisar umurnin ta fara shirye shiryen aikawa da sojojinta da zasu karbi aiyukan wanzar da zaman lafiya daga hannun dakarun kungiya AU a yankin Darfur da yaki ya tagaiyara a kasar Sudan.

Wata sanarwa a yau jumaa ta bukaci sakatare janar Kofi Annan daya fara shirya sojojin ba tare da bata lokaci ba,wadanda ake sa ran zasu hade da dakarun AU a matsayin bangare na dakarun na Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar ta shawarta cewa ya kamata Annan da AU su bada hadin kansu ga gwamnatin Sudan da kuma wadanda suke taka rawar gani wajen kokarin wanzar da zaman lafiya a Darfur.