1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cin hanci da rashawa a yammacin Afirka

November 14, 2022

Hadin gwiwar hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma sun gana a birnin Yamai inda suka yi don duba matsalar a cikin kasashen yankin da ma nazarin yadda za a hada karfafa musayar bayanai.

https://p.dw.com/p/4JVl7
Mai Moussa Basshir na HALCIA da Abdulrashid Bawa na EFCCHoto: DW

A shekara ta 2010 ne kasashen Afirka ta Yamma suka kafa wannan kungiya mai suna RINLCAO da Faransanci ko NACIWA da Ingilishi wacce ta hada hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashe 15 na kungiyar ECOWAS domin hada gwiwar tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, wacce ke zama tamkar ana magani ne kai na kaba a cikin kasashen Afirka.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato EFCC, Abdulrashid Bawa wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma, ya ce za su yi wa aikin yaki da wawurar dukiyar talakawa garambawul, ganin yadda abin ke kara fadi a yankin yammacin Afirka.

Daga nashi bangare shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijar wato HALCIA Mai Shari'a Mai Moussa Basshir ya ce kasashen nasu na hada karfi da karfe a wannan kokowa ta yaki da cin hanci, kamar yadda manyan kungiyoyin irin nasu na duniya suka bukatar da a yi hakan domin cimma matsalar a fadin duniya.

Taron neman kawo karshen cin hanci da rashawa da aka yi a Nijar
Mahalarta taron yaki da cin hanci da rashawa a YamaiHoto: DW

Shugabannin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasashe 15 mambobin kungiyar ta RINLCAO ko NACIWA da suka halarci taron na birnin Yamai, sun fito ne daga kasashen Najeriya da Cote d'Ivoire da Ghana da Guinea Busseau da Saliyo da kuma Togo tare da sauran wasu jami'an yaki da wannan matsala.

Wannan taro na birnin Yamai na zuwa ne a daidai lokacin da a kasashe da dama kamar su Najeriya ake zargin su kansu shugabannin hukumar yaki da cin hancin da karbar rashawa ko kuma yin tsambare a cikin aikin nasu dan dadada wa gwamnatocin da suka kafa su. To sai dai Abdoulrashid Bawa shugaban hukumar EFCC a Najeriya batun ba haka yake ba.

Taron ya kuma sanar da cewa hukumar EFCC a Najeriya ta bude babbar makarantar da za ta zamo cibiyar horas da jami'an yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka ta Yamma a nan gaba.