Ko ka san tsadar kudin haya a Turai? | Zamantakewa | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ko ka san tsadar kudin haya a Turai?

Cikin shekaru 12, farashin kama gidajen haya a Jamus ya yi tashin gwauron zabi a inda aka sami kusan karin kashi 27 daga cikin dari. Ma’aikata musamman wadanda ba Turawa ba na kukan biyan kusan rabin albashinsu.

Tsarin bada gidajen haya a Turai ya sha banban da yadda ake bada su a Afirka. A Turai gidajen haya ana bada su ne bisa wasu ka'idoji wanda ake bukatar mutum ya cika kafin a bashi haya, wanda in har mutum ya cika su kuma ya sami gida mai gidan bashi da damar tada mutum ko da ko rashin biyan kudin hayan ne ko rashin jituwa tsakaninsu ne, masu gidan na iya tada dan haya ne kawai idan suna bukatar wajensu don amfanin kansu ko za su sayar. Wannan dokar na daya daga cikin dalilan da ya sa masu bada gidajen haya ke tankade da rairaya wajen ganin sun tace wa za su ba wa hayar gidansu. A Afirika ka'idar ta kudi ce kawai da zarar mutum ya bada kudi ba a damuwa daga ina mutum ya fito, mene ne sana'ar shi, akasarin lokuta a Afirka babu wata rubutacciyar yarjejeniya tsakanin mai bada haya da mai karba.

Bosnien Herzegowina EU-finanziertes Projekt Roma Action in Kakanj (DW/A. Feilcke)

Akwai dai gida hawa-hawa kowa da bangarensa

A Jamus da ma wasu sauran kasashen duniya da suka ci gaba kudin haya ana biyan shi ne a duk karshen wata wanda hakan ya fi sauki idan aka kwatanta da yadda ake yi a Afirka wanda dan haya sai ya biya kudin haya na shekara daya zuwa biyu. Baya ga nan akwai wani kudin da mutum zai biya (a kalla kudin hayan wata uku) wanda za a aje su ne har sai in mutum ya tashi fita idan akwai abin da ya bata a yayin zaman shi a gidan sai ayi amfani da wannan kudin a gyara idan ya na da canji a bashi abin shi.

 Malam Musa wani mazaunin Jamus ya gwammace da tsadar hayan Turai kan saukin ta Afirka, inda ya ke ganin biyan kudin haya a duk karshen wata yafi sauki kuma a nan mutum na biyan kudi kuma ya na ganin amfanin shi. A cewar shi ba yadda za ai gida ya sami matsala kai wa mai gida magana bai zo ya gyara ba .

" A Afirika kasashe kamar su Gambiya, Najeriya da sauransu masu gida na karbar kudin haya na shekara daya, biyu har uku wanda ya na daya daga cikin abubuwan da ke sa idan wata matsala ta samu a gidan sai dai dan haya ya yi maganin abun da kan shi, mai gida ya karbi kudin shi ba zaka sake ganin shi ba".

Ba wai baki ne kawai ke kukan tsadar kudin haya a Jamus ba har da suma Jamusawan Mr. Reich  da ya kwashe shekaru ya na aiki kuma ya na zaune gidan iyayenshi saboda tsadar kudin haya ya bayyani kamar haka:

Bildergalerie Internationale Studierendenwohnungen (Henny Boogert)

Wasu kan hadu a dakin gambiza su biya kudin tare

" Shekaru uku na fara koyan aikina bani da isasun  kudin da zan iya kama haya wanda dole ya sa na zauna da iyayena har sai daga baya kafin na samu dan karamin gida mai dakuna biyu na daidai karfina."

Matashiya Joy ta tabatar da tsadar kudin haya na daya daga cikin abin da ke ci wa mutane tuwo a kwarya don a wata mutum sai ya kashe sama da rabin albashin shi ma haya.

"Kamar mu a Hamburg idan mutum ya na da albashin euro dubu (misalin dubu 400) ba zai ishe shi ya kama gidan kanshi ba kuma ya yi sauran hidimomi wa kansa, amma akwai gidaje da mutane marasa karfi  ke haduwa su kama sai su raba kudin hayar a tsakaninsu wanda ya fi sauki."