Kira ga Rasha kan hadin kan Ukraine | Labarai | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira ga Rasha kan hadin kan Ukraine

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga mahukuntan Rasha da su mutunta alkawuran da suka dauka domin kawo karshen rikicin Ukraine.

Wannan kira yazo ne bayan da 'yan awaren gabashin kasar ta Ukraine suka zabi shugabanninsu a zabubukan da suka gudanar na shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a jiya Lahadi. Shugaban diflomasiyar kasar ta Jamus ya ce wannan zabe da ke matsayin jeka-nayi-ka a idanun kasashen Turai, zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar da aka cimma a birnin Minsk tsakanin hukumomin na Kiev da na Moscow a ranar biyar ga watan Satumbar da ya gabata. A nata bangaren Rasha ta yi kira ga hukumomin Ukraine da su daina daukar duk wani mataki na soja a yankin gabashin kasar, inda ta ce sababbin hukumomin da aka zaba a wadannan yankuna na da hurumin tattaunawa da hukumomin na Kiev dan samun kwanciyar hankali mai dorewa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu