Kasashe da dama sun yi asarar mahajjata | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe da dama sun yi asarar mahajjata

Rahotanni na nuni da cewa kasashen Iran da Masar da Najeriya na daga cikin kasashen da suka fi yin asarar mahajjata a hadarin da ya afku a Mina a yayin aikin hajjin bana.

Halin da mahajjata suka samu kansu yayin hadarin da ya afku a Mina

Halin da mahajjata suka samu kansu yayin hadarin da ya afku a Mina

Sauran kasashen da suma suka rasa mahajjata sun hadar da Indonesiya da Mali da Indiya da Pakistan da Nijar da Kamaru da Ivory Coast da Chadi da Aljeriya da Somaliya da Senigal. Su ma dai kasashen Moroko da Libiya da Tanzaniya da Kenya da Burkina Faso da Burundi da Netherlands da Benin sun rasa nasu mahajjatan. Kawo yanzu dai mahukuntan Saudiya ba su kai ga bayyana ko 'yan asalin wadanne kasashe ne suka rasa rayukansu a yayin turmutsutsun na Mina ba, sai dai ofisoshin jakadancin kasashen da abin ya shafa a Saudiyan da kuma kafafen yada labarai sun bayar da sanarwar cewa mahajjatan Najeriya 64 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da 244 suka bace, kasar Iran kuwa ta rasa mahajjata 239 yayin da 241 kuma ba aji duriyarsu ba, kana Masar ta yi asarar mahajjata 75 yayin da 94 suka bace.