Kasar Saudiya ta bada shawara ga Lebanon da Syria | Labarai | DW | 17.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Saudiya ta bada shawara ga Lebanon da Syria

Kasar Saudiya ta mika wata shawara ga kasashen Lebanon da Syria game da yadda zasu kawo karshen zaman doya da manja dake tsakaninsu game da kisan tsohon firaminista Rafik Hariri.

Ministan harkokin wajen Saudiya,yarima Saud al-Faisal,yace kasarsa tayi mika wannan tayin kuma ta jiran martani daga kasashen biyu,da suke zargin juna game da kisan tsohon Firaministan.

Kisan Hariri,ya janyo tsamin dangantaka tsakanin makwabtan biyu,musamman ma bayan bincike da aka gudanar, ya nuna cewa da hannun manyan jamian kasar Syria ciki,batu kuma da Syrian ta karyata,haka kuma tace ba zata amincewa masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya su yiwa shugaba Bashar al Asad tambayoyi game da kisan ba,inda tace a shirye take ta fuskanci kasashen duniya akan wannan batu.

A watan oktoba ne dai komitin sulhu ya bukaci Syria da ta bada cikekken hadin kanta ga masu binciken ko kuma a dauki wani mataki da baa baiyana ko wani iri ne ba akanta.