1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya

February 20, 2024

Kungiyar mamallaka manyan motocin da ake safarar man fetur a Najeriya da su na ci gaba da yajin aikin da ta fara a ranar Litinin, lamarin da ya fara haifar da karancin mai a wasu yankuna.

https://p.dw.com/p/4cb9b
Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Kungiyar da ake wa lakabi da NARTO ta ce karya darajar Naira har sau biyu da gwamnatin Najeriya ta yi a kasa da shekera daya ya janyo wa mambobinta asarar da ba za ta iya ci gaba da daurewa ba. Tuni dai aka fara samun rahotannin dogayen layuka a gidajen mai na birnin Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya da ma babban birnin kasar Abuja.

A cikin wannan makon ne dai kungiyar kwadagon kasar ta bukaci 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwatarsu don yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gagarumar zanga-zanga da ke adawa da tsadar rayuwa wacce ke ci gaba da bijire wa matakai dabam-dabam da mahukuntan na Abuja ke dauka.