1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
November 14, 2023

Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya ta bi sahun kungiyoyin kwadagon kasar wajen tsunduma yajin aiki, kan zargin cin zarafin shugaban kungiyar kwadagon da kuma gaza cika yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.

https://p.dw.com/p/4YnkP
Najeriya | NLC | Abuja | Yajin Aiki
Zanga-zangar kungiyoyin kwadagon NajeriyaHoto: Uwais/DW

Al'ummar Najeriyar dai sun wayi gari cikin yajin aikin ne da kungiyoyin kwadagon na NLC da TUC suka fara, inda suka datse hanyoyin samar da wutar lantarki a wasu sassan kasar musamman a manyan birane tare da tilasta kalilan daga cikin ma'aikatan da suka fito aiki shan yajin da suka daka. Kungiyoyin dai na koke ne kan zargin dukan da aka yiwa shugabansu Joe Ajaero da kuma wasu yarjeniyoyin da suka cimma dsa gwamnati, kuma tuni kungiyar malaman jami'o'in kasr da ta ma'aikatan lafiya suka mara musu baya. Matakin nasu dai, ya gurgunta yanayin aiki da ma zirga-zirga ta ababen hawa a wasu sassan Abuja.

Najeriya | Yajin Aiki | Kungiyoyin Kwadago
Kungiyoyin kwadagon Najeriya, sun jima suna yajin aiki don neman biyan bukataHoto: dapd

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka shiga ya sabawa kaida, domin kuwa akwai umurnin kotu da ta haramta shi. Sabawa umurnin kotu dai babban laifi a tsarin dokokin Najeriyar, sai dai duk da haka sun yi biris da umurnin. Mafi yawan ofisoshi a Abuja sun kasance a garkame jami'an kungiyar kwadago sun sa sarka sun rufe kofofin shiga, abin da ya tilastawa ma'aikata shiga yajin aikin na sai abin da hali ya yi. Sai dai kuma, sannu a hankali tasirin kungiyar kwadagon na raguwa a kasar. Duk da dagewa ta amfani da tilasta ma'aikata yajin aikin da alamun tasirin kungiyar na ci gaba da raguwa, saboda matsaloli na wahalhalun tattalin arziki da ma siyasa da ke shiga cikin lamarin.