Kaddamar da shirin tsabtace Ogoni | Labarai | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kaddamar da shirin tsabtace Ogoni

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a bikin bude aikin fara tsabtace yankin Ogoni da ke Niger Delta mai arzikin mai.

Yankin Ogoni na Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya

Yankin Ogoni na Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya

Wakilcin na Osinbajo dai na zuwa ne biyo bayan soke halartar bikin mai cike da tarihi da Shugaba Buhari ya yi. Har ya zuwa yanzu dai shugaban Najeriyar bai ba da wani dalili ba kan abin da da ya hana shi halartar bikin. Aikin tsabtace muhallin na Ogoni za a yi shi ne a kan kudi dalar Amirka biliyan daya. Tuni dai aka kara tsaurara tsaro a yankin na Niger Delta, sakamakon masu tada kayar bayan yankin da ake wa lakabi da Niger Delta Avengers, inda hare-haren da suke kai wa ke nema ya kara kassara tattalin arzikin kasar. Cikin watan Agusta na shekara ta 2011 ne dai Shirin Kare Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), ya bayyana cewa yankin Ogoni ka iya bukatar shirin tsabtacewa mafi girma da aka taba yi a duniya, biyo bayan malalar danyan mai da yankin ya fuskanta.