1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya yi watsi da takardar takara a APC

May 10, 2022

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi watsi da batun saya masa takardar neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC da aka ce wasu 'yan arewa suka yi.

https://p.dw.com/p/4B5y4
Nigeria | Präsident Goodluck Jonathan
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

A ranar Litinin ne labarin saya wa Jonathan da aka sani a jam'iyyar Adawa ta PDP fom din APC ya karade shafukan sada zumunta, abin kuma da mai magana da yawunsa Ikechukwu Eze ya karyata cikin wata sanarwa.

'Yan siyasar Najeriya dai sun yi kaurin suna wajen sauye-sayen jam'iyyu a lokacin da zabe ke kawo jiki.

Wasu dai na mamakin yadda jam'iyyar APC za ta amince da Goodluck Jonathan a yanzu, mutumin da ta bayyana shi a matsayin wanda ya gaza a baya.

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari zai kammala wa'adinsa na mulkin shekaru takwas a badi, wadanda ke son su gaje shi sama da mutum 20 ne suka sayi takardun neman takara, daidai lokacin da jam'iyyar APC ke cewa za ta rufe cinikin takardun a ranar Talata.