Jefe-jefen da akewa ′yan PDP a Najeriya | Labarai | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jefe-jefen da akewa 'yan PDP a Najeriya

A taron da ta gudanar har ta fitar da sanarwa, Jamiyyar PDP mai mulkin Najeriya ta nuna damuwa a kan yawan jefe-jefen da akewa shugaban kasar, yayin yakin neman zabe.

Jamiyyar ta bayyana hakan ne a taron ‘yan jaridu a Abuja, inda tace yin hakan wani nakasu ne ga demokradiyyar wannan kasa, inda hakan na faruwa ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan takarar manyan jamiyyun kasar na PDP da APC suka sawa hannu, abinda ke daga hankulla saboda yiwuwar fuskantar rigingimu a zaben kasar. Ayarin shugaban na Najeriya dai ya fuskanta matsalar jefe-jefe a jihohin Katsina Bauchi Taraba da ma Adamawa a ci gaba da yakin neman zabe da yake yi a kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba