1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jita-jitar kai sojan hayar Rasha a Mali, sabon nau'in Corona

Usman Shehu Usman MNA
September 17, 2021

Kasashen Turai sun yi barazanar janye dakarunsu daga Mali, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya malaman addinai sun yunkuro don magance rikicin addini, an yi hasashen cewa Afirka ka iya zama tungar sabon nau'in Corona.

https://p.dw.com/p/40TAV
Mali Premierminister Choguel Kokalla Maïga
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst des Premierministers von Mali

A wannan makon da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung za mu bude sharhunan jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka. Jaridar ta ce jita-jitar kawo sojojin haya na Rasha a kasar Mali ya yi kamari. Sai jaridar ta ci gaba da cewa kasashen Jamus da Faransa sun yi barazanar janyen dakarunsu daga kasar Mali muddin rade-radin da ake yi ya tabbata. Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer, ta yi barazanar cewa za a kawo karshen zaman sojojin kasashen Turai da na Majalisar Dinkin Duniya baki Daya a Mali, har da wadanda ke aikin ba da horo ga sojojin Mali. Domin a cewar Bajamushiyar idan sojojin da ke mulki a Mali suka kulla yarjejeniya da Rasha haka ya saba wa kudurin da aka kulla da Jamus da Faransa da Tarayyar Turai har ma da Majalisar Dinkin Duniya.

Daya daga cikin kwamandojin kungiyar Anti-Balaka Kanal Goumou Passy a Afirka ta Tsakiya
Daya daga cikin kwamandojin kungiyar Anti-Balaka Kanal Goumou Passy a Afirka ta TsakiyaHoto: DW/A. Kriesch

Yanzu kuma sai Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda wasu shugabannin addinin Krista da na Islama suka daura damar kawo karshen rikicin addini. Wannan labarin ya fito a jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce wani Kardinal da Limami sun hada kai wajen kawo zaman lafiya. A jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ana samun fadace-fadace tsakanin musulmai da kristoci, wannan rashin jituwar ita ce manyan shugabannin addinin suka daura damar magancewa. A cewar shugabannin addinin, ta yaya kasar da ba ta wuce shekaru 50 da aka samu 'yancin kai ba, amma al'ummarta da talauci ya yi wa kanta suke kai wa juna farmaki, duk da cewa su 'yan kasa daya ne.

Ma'aikaciyar jinya tana karbar allurar riga-kafin Corona a Afirka ta Kudu
Ma'aikaciyar jinya tana karbar allurar riga-kafin Corona a Afirka ta KuduHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Ita kuwa Jaridar Bild ta yi labarinta ne kan cutar corona, inda ta ce wani bincike da kwararrun kasar Amirka suka yi a kasashen Afirka 20 ya nuna cewa nahiyar na iya zama wata tungar sabbin nau'o'in corona. Sakamakon binciken ya gano cewa akwai matukar rashin ba da alluran riga-kafin COVID-19 a nahiyar Afirka. Wasu kasashen ba su samar da wadatattun alluran ba ga kuma yadda har yanzu ake kyamar allurar tsakanin al'ummar Afirka. Kuma bincike ya nuna cewa kasashen da ake samun karancin riga-kafi a nan ne ake samun bullar sabbin nau'o'in cututtuka da ke da alaka da corona.

Idan muka leka kasar Gambiya za mu ji cewa gwamnatin kasar ta fara kin karbar 'yan gudun hijira. Jaridar die Welt ta ce ba Gambiya ce kadai ta fara daukar wannan mataki ba, akwai wasu kasashen Afirka da su ma suka fara daukar irin wadannan matakai. A cewar jaridar wani bincike da ta gudanar ya gano cewa wannan sabuwar siyasa ce da yanzu haka wasu kasashen Afirka suka fara yi, yayin da su kuwa kasashen Turai ke kokarin takaita kwararar bakin haure cikin kasashen na Turai.