Japan za ta sanya wa Korea Ta Arewa takunkumi. | Labarai | DW | 19.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Japan za ta sanya wa Korea Ta Arewa takunkumi.

Ƙasar Japan ta ce za ta sanya wa Korea Ta Arewa takunkumin tattalin arziki, a wata mai zuwa bayan wani ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ya bukaci Korean da ta tsai duk gwaje-gwajen rokokin da take yi.

Jami’an gwamnatin Japan ɗin dai ba su bayyana yadda takunkumin zai kasance ba ko kuma lokacin da zai fara aiki.

Amma wata kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce Japan za ta ɗora hannu ne kan duk kadarorin Korea Ta Arewan da ke ƙasarta, kuma za ta hana aikewa da kuɗaɗe zuwa Korean tun daga wata mai zuwa.