Janna´izar sojojin Jamus da suka mutu Afganistan
April 24, 2010Talla
Dubun-dubunan jama´a ne suka halarci jana´izar sojojin Jamus huɗu da ´yan Taliban suka kashe a ƙasar Afganistan yau kwanaki tara da suka wuce.
An gudanar da wannan jana´iza a birnin Ingolstadt tare da halartar shugabar gwamnati Angela Merkel, da ministan harakokin waje Guido Westerwelle.
Da yake bayyani a wurin jana´izar, ministan tsaro Karl Theodor zu Guttenberg ya zana sunayen sojojin tare da yi masu godiya da jinjina damste, a matsayin
gwarzayen ƙasar Jamus.
A wannan wata na Afrilu kaɗai sojoji bakwai suka rasa rayuka a Afganistan.
Daga shekara 2001 zuwa yanzu, jimlar dakarun Jamus da ´yan taliban suka hallaka sun tashi 43.
Mawwalafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Zainab Mohamed Abubakar