Jamus za ta tura sojojin kasar arewacin Iraki | Labarai | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta tura sojojin kasar arewacin Iraki

Majalisar ministocin Jamus ta amince da wani kuduri da ya tanadi tura sojoji 100 zuwa yankin arewacin Iraki, don horas da sojojin Kurdawa da ke yakar kungiyar IS.

Merkel und Leyen Bundeskabinett 13.08.2014

Shugabar gwamnati Angela Merkel da Ministar tsaro Ursula von der Leyen

Gwamnatin Tarayyar Jamus ta share fagen aikin horaswa da rundunar sojin kasar ta Bundeswehr za ta yi a arewacin Iraki. Yanzu haka dai majalisar ministocin Jamus ta amince da wani kuduri da ya tanadi tura sojojin Jamus 100 zuwa yankin, inda za su horas da sojojin Kurdawa da ke yakar masu Jihadin na kungiyar IS.

Sai dai kudurin bai ba da damar shigar da mayakan Jamus cikin fadan ba. Yanzu dole kudurin ya samu amincewar majalisar dokoki. Tun a lokacin bazara Jamus ke taimaka wa kungiyoyin Kurdawa na Peshmerga a fafatawar da suke yi da mayakan kungiyar IS. Kasar ta aike da makamai da sauran kayan aikin soji.