Kurdawa mutane ne da ke zaune a wasu yankuna na kasashen da suka hada da Turkiyya da Iraki da Siriya da kuma kasar Iran.
Bisa ga kididdiga da aka gudanar, akwai kimanin Kurdawa miliyan 30 a duniya yanzu haka kuma galinsu na zaune ne a kasar Iraki. Rahotanni na cewar sama da miliyan guda sun yi kaura zuwa kasashen yamma ciki kuwa har da Jamus inda kimanin dubu 700 ke zaune.