1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan bindiga ya kashe mutum uku a Paris

Abdullahi Tanko Bala
December 23, 2022

A kalla mutane uku suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka sami raunuka a harin da wani dan bindiga ya kai cibiyar al'adu ta Kurdawa a birnin Paris.

https://p.dw.com/p/4LNym
Paris Schießerei in Innenstadt
Hoto: JULIETTE JABKHIRO/REUTERS

Masu bincike basu baiyana manufar maharin ba. Sai dai an taba tuhumar sa da aikata tarzoma da nuna wariya.

Tuni dai aka kama maharin wanda ya sami raunuka a fuskarsa kamar yadda wani mai gabatar da kara ya shaidawa 'yan jarida a wurin da lamarin ya faru.

Lauyan cibiyar al'adun ta Kurdawa da aka kai wa hari yace dukkan mutanen da aka kashe Kurdawa ne kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Masu gabatar da kara sun kaddamar da binciken kisan kai da kuma tada tarzoma.