Jamus za ta janye jami'anta na diflomasiyya daga Nijar
March 21, 2026
Talla
A sakon da ta wallafa a shafinta na intanet, ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce, sakamakon hali na matsalar tsaro za a sauya wa offishin jakadancin Jamus da ke Yammai mazauni zuwa wajen birnin. Jamhuriyar Nijar da ke karkashin mulkin soji a yanzu, ta dade ta na fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai da suke da alaka da Al-Qaeda da kuma IS.
Karin bayani:Nijar: Matsalar tsaro na kamari a yankin Sahel
Ma'aikatar ta Jamus ta ce, 'yan ta'adda sun fi farautar 'yan kasashen waje a kai hare-harensu da kuma yin garkuwa da su. Ko a watan Janairun wannan shekarar, Amurka ma ta bukaci ma'aikatanta da ba sa yin aikin gaggawa da su fice daga Nijar din saboda halin tsaro.