Jamus ta tsaurara matakan yaki da corona | Labarai | DW | 27.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta tsaurara matakan yaki da corona

A wani yunkuri na rage karuwar da cutar corona ke yi a Jamus, shugabar gwamnati Angela Merkel ta gana da gwamnoni 16 da ke kasar domin daukar matakan yaki da cutar a kasar.

Angela Merkel dai na mai goyon bayan saka haraji na Euro 50, kwatankwacin Naira dubu 22, ga duk wanda aka kama ba ya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a bainar jama'a. Har wayau tana mai bukatar saka dokar rage yawan taron mutane a cikin gida da ma waje.

Shugabar gwamnatin ta ce tana goyon bayan ministan lafiya da ya bukaci a daina gwajin cutar kyauta ga masu dawowa balaguro daga ketare.

A baya dai Jamus ta yi nasarar shawo kan annobar amma bisa janye dokokin da suka sanya a farkon shekarar nan ana yawan samun sabbin kamu da cutar a yanzu haka.