1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta samu karuwa ta fuskar fitar da kayayyaki

November 8, 2025

Wasu rahotanni na hukuma a kasar Jamus, sun nuna cewa an samu karuwa a fannin fitar da kayayyaki da ake kerawa daga kasar a karo na farko tun cikin watan Yunin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/53JPb
Hoto: Patrik Stollarz/AFP/Getty Images

 

Jimillar adadin kayayyaki da ake fitarwa ta karu da kashi 1.4 cikin 100, zuwa euro biliyan 131.1, kwatankwacin kusan dala biliyan 151 a watan Satumba, abin da ya zarce hasashen masana tattalin arziki.

Wannan karuwar ta zo ne watanni biyar a jere da ake samun raguwar fitar kayayyakin da ake sarrafawa a Jamus, duk da cewa adadin bai kai na watan Satumbar bara ba.

Fitar kayayyaki zuwa Amurka ta tashi da kusan kaso 12 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Sai dai fitar kayayyaki zuwa kasar China ta ragu da kaso2.2 cikin 100 a watan Satumba, abin da ke nuna raguwar bukata da kuma karin gasa daga masana'antun cikin gida na kasar ta China.

A gefe guda kuma, shigo da kaya daga kasar Chinar ne ya karu a Jamus din da fiye da kashi 6 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Agusta, abin da ya sanya kasar ta Sin ta zama babbar tushe ta kaya ga Jamus a wannan watan.