1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kama masu yi wa Rasha leken asiri

April 18, 2024

Masu gabatar da kara a Jamus sun ce 'yan sanda a jihar Bavaria sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yi wa Russia leken asiri.

https://p.dw.com/p/4evxl
Yan sandan wajen binciken ababen hawa
Yan sandan wajen binciken ababen hawaHoto: Revierfoto/Revierfoto

Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa mutanen biyu akwai kasancewa a matsayin masu yin zagon kasa da kuma lalubo yadda za a dasa ababen fashewa kamar yadda ofishin masu gabatar da karar na Jamus a birnin Kalsruhe suka bayyana.

Karin Bayani: Tsamin diflomasiyya tsakanin Jamus da Rasha

Har'ila yau Jamus ta gayyaci jakadan Rasha a birnin Berlin bayan kamen don karin bayani.

'Yan sanda sun binciki gidajen mutanen da kuma wuraren ayyukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake tuhuman sun rika neman wurare da za a iya kai wa hari ciki har da sansanin sojin Amurka da ke Jamus.