1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
June 8, 2022

Mahukunta a Jamus sun sha alwashin ci gaba da tallafa wa kasar Ukraine a yakin da suke yi da Rasha. A kokarin kawo karshen yakin da ma matsalar karancin abinci da yanzu haka duniya ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4CQUH
Litauen Besuch Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky a wannan Laraba, ya tabbatar masa da ci gaba da taimaka musu a yakin da suke yi da Rasha wanda aka kwashe sama da kwanaki 100 ana gumurzu.

Kazalika shugabannin biyu sun kuma tattauna batun yiwuwar fitar da tarin hatsi da ke Ukraine ta cikin teku, a cewar kakakin gwamnati.

Matakin rufe tashoshin ruwan Ukraine da Rasha ta yi ne musabbabin karancin abinci da yanzu haka duniya ke fuskanta da ma karin farashinsa musamman ma a nahiyar Afirka.

Mista Scholz ya kuma sanar da Zelensky tattaunawar da ya yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma shugaban Rasha Vladmir Putin.