1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta hana Ukraine makamai masu linzami

Abdullahi Tanko Bala
March 14, 2024

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta kada kuri'ar kin amincewa da tura manyan makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa Ukraine a yakin da ta ke cigaba da yi da Rasha.

https://p.dw.com/p/4dWTi
Marschflugkörper Taurus der Bundeswehr
Hoto: picture alliance/dpa/Bundeswehr

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta kada kuri'ar kin amincewa da tura manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango zuwa Ukraine a yakin da ta ke cigaba da yi da Rasha.

Jam'iyyar adawa ta CDU ta bukaci bai wa Ukraine makaman samfurin Taurus masu cin dogon zango domin taimaka mata ganin yadda Rasha ke kara samun galaba a yakin

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce za a iya tura makaman ne kawai tare da sojojin Jamus na Bundeswehr da za su sarrafa su amma yin hakan zai jefa Jamus cikin da Rasha.

A waje guda dai shugaban kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg a rahotonsa na shekara da ya gabatar ya yi kira ga kasashen kawancen su kara himma wajen taimaka wa Ukraine.