Jamus ta gargadi Turkiya kan Siriya | Labarai | DW | 02.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta gargadi Turkiya kan Siriya

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya gargadi mahukuntan Turkiya dangane da tsawaita kasancewar dakarun sojojin kasar a Siriya.

Dakarun Turkiya na kutsawa kan iyakar Siriya

Dakarun Turkiya na kutsawa kan iyakar Siriya

Steinmeier ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce duba da yadda Turkiyan ta zage dantse a 'yan kwanakin baya-bayan nan wajen kai hare-hare a Siriyan biyo bayan kaddamar da yaki da 'yan ta'addan IS da mahukuntan na Ankara suka yi, a yankunan da ke kan iyakar Turkiyan da Siriya akwai damuwa, yana mai cewa sun damu matuka wajen ganin an kaucewa tsawaita dadewar ayyukan sojojin kasashen ketare a kasar ta Siriya. Akwai dai korafin cewa Turkiyan na amfani da wannan dama wajen kai hare-hare kan mayakan Kurdawan na YPG a Siriyan.